Thursday, August 19, 2010

KTSU MAIN GATE

YAR'ADUA VERSITY EMBARKED STRIKE IN KATSINA

The academic Staff union of Universities of the Umaru musa Yar’adua University katsina state has commenced a two week warning strike to actualise their demand for increase in salary.
The Chairman of the union,comrade Usman Abdullahi stated this while addressing a press conference in katsina.
Comrade Usman abdullahi said upto now the state government has refused to pay adequate attention to their demand which compelled the union to commence the warning strike today.
He said the union resolved to pursue for the full implementation of ASUU and FGN agreement in the instutition.
Comrade Usman abdullahi said going by the terms of employement between the state government and the member of the union as well as the benchmark for establishing a university in Nigeria as approved by the federal government, the union has categorically rejected the persistence of the state government to partially and unilaterally implement the FGN and ASUU agreement without recourse to laws of katsina state that was tantamount to the breach of the employement contract and violation of the laws of katsina state.
Comrade Usman Abdullahi called on the state government to fully implement the said agreement effective from july 2009.
All efforts to get the special adviser to the governor on Higher Education, Alh Adamu Mato Zango who was sighted by the reporters refused to comment, who later use the backdoor of his office and left the reporters stranded only to be told by the public Relation Officer that the adviser will invite them later for briefing on the state government’s position on the strike action.

HOTON ALH SABO MUSA KATSINA

MARTANIN DA ALH SABO MUSA YA MAYAR MA 'YAN CPC A KATSINA

wannan ita ce tattaunawar da wakilinmu da ke katsina ya yi da shugaban kungiyar tuntuba akan sake tsayawa takarar Gwamnan jihar katsina Barista Ibrahim Shehu Shema a katsina.
Alh. Sabo Musa yana daga cikin manyan 'yan siyasar jihar katsina yanzu,ya fadi dalilin kafa wannan kungiya ta so mai suna Shema partinership, sannan ya maida martanin akan zargin da jam'iyyar CPC ke yiwa Sarakunan katsina da jam'iyyar ta CPC ta ce sun atsoma baki cikin al'ammuran siyasar katsina, dama wasu bayanan ga yadda hirar take:
KH:Sabo musa kayi man bayani dalilin kafa wannan kungiya ta ku da kake yi wa jagoranci. Wanda kuma an kafa ta ne domin a ga gwamna Shema ya sake cin zabe a shekarar 2011?
SABO MUSA: gaskiya kamar yadda ka sani makasudin kafa wannan kungiya don mu sakawa shi gwamna, bisa ayyukan alherin da yake gabatrwa a jihar ta katsina. Ya kamat duk wani mai kiyasa a katsina, yasan irin abin da Shema ya yi wannan ne yasa muka hadu muka kafa wannan kungiya domin yin wani abu da zai nuna masa cewa mu mutanan katsina mun ji dadin abin da ya yi. Sannan mun lura gwamnati tana aiki amma mafi yawancin mutane ba son abin da ake ciki ba.
Dalili ba biyu shi ne akwai wasu 'yan mara sa kishi duk da cewa sun shiga gwamnati sun tara kudi, amma kuma ba su son irin abin da shi gwamna shema yake a karkashin gwamnantin shi saboda hassada, suna ganin su yakamata ace suke yi kuma ba su ke yi ba. Sai suka rika amfani da dukiyar suna haddasa fitinu. Wannan yasa duk lokaci da suka soke shi mu rama idan sukai masa sharri mu nunwa jama'a wannan abun ba haka yake ga yadda yake.
Abu na uka kuma shi ne, za mu son ya cigaba da zama gwamnan jihar katsina, idan aka samu can jin gwamnati mun shiga cikin wani irin hali, saboda irin abin da ya yi ba a taba samun gwamnan da ya iske aiki sai da ya ida sannan ya cigaba da na shi, ka ga hanyoyi da ya fara yin wadanda za su kewaye gari, ga kuma gidaje da ya gina idan har aka samun can jin gwamnati ana iya kashe irin wadannan manyan ayyuka. Bayan haka ga wasu ayyukan wadanda suna da matukar amfani ga jama'a, misali kamar Asibitin Turai yar'duwa da kuma Asibitin Kashi wanda masana suka ce duk Afrika babu irin ta, ga motocin tafi da gidanka wanda da amurika da finafinai kadai muke ganin su, hatta mutanan da ke cikin karkara suna afmana da wannan garabasa.
KH: To, amma sai gashi wasu 'yan siyasa suna ganin abun ba haka ne ba, ya yarda wasu 'yan siyasar da aka fara tafiya tare, wanda har wasu daga ciki suka fice daga PDP zuwa ta jam'iyya?
SABO MUSA: Wannan ba gaskiya ba ne, yau idan an kyautatama al'ummar jihar katsina ba a kyautatama wasu da ke tare da gwamnati ba anyi laifi? Saboda haka ita gwamnati ta al'ummar jihar katsina ce baki daya, tunda gwamnati ta al'ummar jiahar katsina ce idan aka kyautattawa wani ba a kyautattawa wani ba, ba a laifi ba. Wadanda suka bar jam'iyyar PDP suka kuma wata daman ba su yi ma jam'iyyar komi, duk wanda ke cikin PDP yake ya da manufar ta ba wata bukata tashi ta kashin kansa ba yana nan bai bar PDP ba.
KH: Gashi jam'iyyar CPC na zargin Sakunan katsina da tsuma baki cikin al'ammuran siyasa, musamman akwai wani sarki da ya nuna jam'iyyar da yake wane martani za ka maida akan wannan?
SABO MUSA: Ace Sarakunan mu suna jam'iyyu wannan cin mutunci masarautar mu ne da Sarakunan mu, wannan cin fuska ne ya kamata a daina. Sarakuna iyayen kasa ne, ra'ayi kuwa duk dan adam yana da na shi, yana son wane ya ci zabe, yana son wane saboda ayyukan alherin da yake ya zarce, saboda haka ra'ayi da ban siyasa da ban. Yau idan iyayen Sarakuna ba su ce Shema ya kyauta ba ai masu yi masa adalci ba, saboda ya kyauta din ya fito da mutuncin jihar katsina, ba a taba taimakon alhazai yadda ya kamata ba sai lokacin Shema, ba wata gwamnatin da ta taba gina masalatai da makarantu da kewaye makabarto ba kamar Shema, wannan aikin Sarakuna ne to sai gwamnati ta zo tana yin wannan don mi ba za su yabawa wannan gwamnati ba. Sannan ina kira ga kungiyar ma'aikata kadda su yarda ayi amfani da su, ko ace su nemi karin albashi, ko karin karamar hukuma ko neman jiha, sannan kadda a cuci ma'aikata amma kuma kadda su kuma su matsa su ce kan su suke so. Kamar ma'aikatan Asibiti da suka tafi yajin aikin ai ba su yi mutunci ba, ina kira a gare su da suji tsoron Allah shi aiki ba ana yin ba ne don albashi kawai, ana yin sa don taimako da samun lada. Saboda haka wancan kiraye-kiraye na CPC wannan abin je farwa ne, babu hujja babu ma'ana.
KH: To a karshe wane kira za kayi ga 'ya 'yam Jam'iyyar PDP su ga sun hada kawunan su domin gwagwarmaya mai zuwa a wannan zaben?
SABO MUSA: Mu 'yan jam'iyyar PDP kan mu hade yake, daman wadanda suke gefe suna ganin abin alheri ne garesu akafa wata gwamnati ai sun sa irin abin da suka aikata a kafa gwamnati su gani mana, yau mutanan nan duk abin da muke cikin gwamnatin nan da su muke ba su taba cewa PDP bata da gaskiya ba, sai yanzu ne za su zo su fadi yanzu ne PDP ba ta yi gaskiya? Bayan sun shiga gwamnati sun debi kudin jama'a to su maido ma gwamnati kudin ta mana, kuma ka tuba ba za kara yin abu be shi ne sharadin tuba, idan kuma kudi ne na wasu ka diba to ka maida masu kudin su sannan ka tuba. Saboda haka a karshe ina kira ga jama'ar jihar katsina gwamna shema ya yiwa mutane abin da ya da ce, mu fito mu saka mashi, duk farfaganda da wasu mutane keyi ku auna nagartar wadanda suka fito takara a wasu jam'iyyun ku gani mana, kuma sai ma ranar zabe za a kara ganin bambamcin shema da sauran.

HIRAR MASARI AKAN KOMARWARSA CPC A KATSINA

KH: A da kana jam'iyyar PDP wanda kuma kana da matukar tasiri, sai gashi lokaci guda ka kuma CPC babu shakka ba za ka rasa dalili ba?
MASARI: To da farko dai kamar yadda jam'iyar PDP ta gudanar da zaben ta a 2006 ta kuma fitar da 'yan takarar ta duk kasar Najeriya, yadda kuma sauran jam'iyyu suka bi sawun yadda jam'iyyar PDP ta yi na kama karya. Bayan mun sauka muka ce to ya kamata mu bullo da wata hanya wadda za ta gyara tsarin mulki da zai fidda zababu bi sa ka'ida, har ma akwai wata kungiya da muka kafa G20. To mun yi kokari a wannan lokacin manyan ta matsa har aka zo aka yi convension har aka gyara wasu al'amurra na tsarin mulki wanda za su fitar da ciyaman na kwamitin amintattu.
To amma wadanda suka amshi mulki sai suka fi da lalacewa, a hankali- ahankali tun wurin zaben muka ga abinda ba su mukayi tsammani ba, bayan an aje akwatina sai daga baya aka ce wai anyi yarjejeniya duk sun ci ni kuma na san zaben shugaban kasa kan shi ko mutun daya ne ya fito sai an je fasa kuri'a idan ku ce ba su san shi to dole a canza dan takara amma wannan karan a jam'iyyar PDP mai mako ta bada mafita sai ya kasance ita ce ma matsalar, sai ka ga gwamnoni sun dauke aikin jam'iayya, idan gwamnoni suka fito suka ce zasu yi kaza sanna sai shugabanin jam'iyyar PDP su ce to, sai ya kasance wutsiya ita ke kada kare ba kare ne ke kada wutsaya ba.
KH: Yanzu idan na fahimce ka, dalilin da yasa kuka bar wannan jam'iyyar kamar kuna babu adalci acikinta ne yasa kuka barta?
MASARI:Absolute. Duk hanyoyin da muka bi wanda zai kawo tsarin da zai yi adalci acikin maganar na karshen nan shi ne wanda muka kawo sauran gwamnoni da yaran su da ke c ikin jam'iyyra suka watsar, kuma ya kasance nine gaba-gaba wajen wannan gyara, gyara bai yi nasara ba, shi ya sa nayi abin da ya dace dole idan da zan bar PDP ne saboda abinda aka yi min da na bari tun shekara hudu da suka wuce, amma ban bari ba.
KH: Amma me yasa ka zabi komawa jam'iyyar CPC duk da cewar akwai wasu jam'iyyun da dama?
MASARI: Ita jam'iyyar CPC wadanda suka kafa ta, irin matsalolin da muka fuskanta a jam'iyyar PDP suma irinta suka fuskanta a jam'iyyar su suka bar ta suka kafa CPC mai akida, wanda kuma mu akidar muke son a bi, saboda haka idan ace ga ka'idar jam'iyya na bi, aka zo akayi jarabawa a matsayin 'yan takara ni da kai, ta nuna jama'a sun fin sonka shi kenan sai in mara maka baya, ai daman ga ka'idar, amma da rana kiri-kira aka baka kuma daga baya ace in zo in bika ai abin ya zama bauta kuma ni na gaji da ita.
KH: Amma gashi ita wannan jam'iya sabuwar jam'iyyar ce, ka na ganin alamun zata yi tasiri a siyasar Najeriya?
MASARI: Ba yawan jama'a sune kasuwa ba? Kai ka ga taron da akayi anan, ka ga motoci da mutanan da suka zo tunda daga sabuwa har Mai'adua, ka gani ko? Indai ba PDP za ta yi kwace ba, kuma a wannan karon ka ji abin da mutane suka ce sai dai akwata bisa ran su.
KH: Misali yanzu kana da wani ra'ayi na tsayawa takara, ko ba ka kai ga yanke shawara ba?
MASARI: Gaskiya yanzu ban yanke wata shawarar tsayawa takara ba.

HOTON DAKTA MUSTAPHA INUWA

TATTAUNAWAR MU DA DAKTA MUSTAPHA INUWA, TSOHON SAKATAREN GWMANTIN JIHAR KATSINA AKAN KOMAWARSA CPC

Tambaya: Dakta Mustapha da farko za mu so muji dalilin ficewarka daga jam'iyyar PDP?
DAKTA: To, dalilin dai kamar yadda muka sha fada wurare daban-daban shi ne rashin adalci da gwamnan jihar katsina Ibrahim Shehu Shema da makarabansa suke yi, a yadda suke tafiyar da harkokin jam'iyya da ita kanta gwmanatin jihar katsina.
Jam'iyya dai ya kamata ace ta kowa-da-kowa ce shi yasa ake ce mata PDP power, amma sai muka ga an maida Shema political Party saboda an zo an zauna duk wani wanda yana da hannu wajen haihuwar jam'iyyar da kuma raya ta ta hanyoyi da dama daga 1998 zuwa yau amma Shema ya zo ya nuna baya bukatar shi ya jawo wasu mutane ya ce sune za su? tafiyar da harkokin siyasa. Ya zo ya rushe kwamitin zartarwa na jam'iyya tun daga matakin gunduma har zuwa jaha, ya na da wadanda ya ga dama acikin ofis din shi, to wanna yasa muka nuna ba mu yarda ba, ba taimako bane ga jam'iyya, a rushe ayi kamar yadda doka ta tsara, sannan muka bi duk matakin da ya kamata mu bi anan jiha muka kai koke tarayya, daga karshe ta tabbata ba, sai muka fahimce Shema nema yake ya kashe jam'iyyar PDP mu kuma ba za mu so a kashe ta ba muna ciki.
Dalili na biyu shi ne ita dai jam'iyya amfanin ta idan an kafa gwamnati to ta taimaka ma jama'a, musamman alkawarin da aka dauka lokacin zabe, da dama Shema muka zagaya muka roki jama'a domin a zabe shi za a yi masu ayyuka na alheri, wadanda suka shafi kowane bangare, sai mu ka ga shi Shema ba wannan ya da me shi ba sai manyan ayyuka musamman hanyoyi har da inda ba a bukatar hanya.
An bar mutane babu ruwan sha, babu magani, makarntu daliban sun koma almajirai, an ki daukar malamai, musamman na karkara an sa kananan hukumomi sun gina an ki daukar ma'aikata, sai mu ka ga babu dalilin da sai sa mu ba wannan gwamnati goyan baya, to sai muka bai kamata ba mu cigaba da zama cikin wannan jam'iyya saboda babu wani aiki da a ka yi wa jama'a ba re aba da misali da shi har a sake zabar ita wannan jam'iyya, to wannan da ma wasu dalilai da dama ya sa muka fita daga PDP.
TAMBAYA: Ba ka gani irin manyan ayyukan da ya yi kamar yadda kace; kamar hanyoyi da gidaje da ya yi wanda har ana ta bashi kyaututika, ba ka ganin wannan nasara ce wanda kuna iya duba al'amarin?
DAKTA: Su wa? Wadanda suka san matsalolin mutanan katsina koko? Wadanda suke bada irin wadannan kyaututikan idan ka bincika ba wanda ya taba zuwa katsina, wadannan kyaututinkan biya ake ana bada so da daman su, kuma kyautar da ya amsa ta farko ba ta aikin sa ba ce, akin da mukayi ne na farko domin an bata ta ne 2006 ba ta shi ba ce ya karba amma daga lokacin zuwa yanzu wace kyauta ya karba? Amma a zahiri mutanan da ke katsina su suka son halin da ake ciki, yanzu idan ka je asibiti ba magani lokacin gwamnatin da ta shude ana sayen magani na Naira miliyan dari hudu, amma yanzu na miliyan arba'in ake saye, gashi ba ruwan sha ba a dauke ma'aikata aiki ba.
Ga shi kananan hukumomi ba sa iya komin sai abinda gwamnatin jiha ta ce masu, komi Ciyaman zai yi sai ya neman izini a jiha kuma daga can za a bashi dan kwangilar da zai yi aikin, amma maida kusan mutun biyu sune ke yin kwangilar ayyukan kananan hukumomin jihar katsina, magana ce ta gaskiya sai dai mutane ba su son a fadi domin tsoro ko wani dalili, ko su Ciyamomin tsakani da Allah ba su jin dadin wannan gwamnati suke ji ba, an maida kamar almajirai saboda babu wani aiki da suke, kuma za ka ga kananan hukumomi suna samun kudin da basu kasawa miliyan ashirin ba bayan sun biya albashi amma me ake da su? Dan abin da za a ba su daman da ta so kishirwar sun wawure. Maganar ace ana bashi award a je 'yan Abuja su zabe shi, idan kuma maganar zabe ne kai ka sani mutane sun gaji da gwamnatin shehu ba za su sake zaban ta ba.
TAMBAYA: To, mutane da yawa suna ganin shigowar ku CPC ya yi za kuyi ku amshi wannan gwamnati?
DAKTA: To, ba jama'a ke zabe ba? Insha'Allahu jama'a za su zabe gwamnatin CPC kuma ba wai jihar katsina kadan ba, daman su ke zabe.
TAMBAYA:Kana ganin yanayin zaben zai canza ganin yadda ake zabe a baya?
DAKTA: Karma ya canza, mutane su za su canza shi da kan su, ace wai anyi sabuwar doka duk wannan ba shi bane, in jama'a na son su ci zabe za su ci, ai anyi anan jihar ba wainsaia anje nisa ba, anan katsina 2003 anyin zabe mun fadi, Sanatoci biyu muka rasa cikin uku, 'yan majalisa takwas muka rasa cikin sha biyar, inda zaben farko aka fara anan jihar na gwamna Umaru da baiyi second term ba, kuma wahalar da mutane suke cikin yanzu ita ta sa suka ce ko za su mutu sai dai mutun amma sai sun tsare mutuncin su a wannan karon daga wannan wulakantatar gwamnati.
TAMBAYA: A karshe wane kira za ka yi ga masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro da kuma ita kanta hukumar zabe ta kasa domin tabbatar da anyi zabe cikin adalci da lumana?
DAKTA: Ni kira zanyi ga dukkan jama'a, musamman sakunan mu da suka zu bar ma kansu da mutunci, suna abinda yake mutane fa ba su jin dadin sa, ya kamata su tsare mutuncin su, su tsare girman su, su dauke kowa na su ne, duk wanda Allah yasa aka zaba to na su ne, amma ace sakuna suna bada umarni kiri-kiri suna ga ya ma jama'a ga gwamnatin da suke so, to wannan kuskure ne.
sannan akwai jami'an hukumar kananan hukumomi suna za ga yawa suna gaya wa mutane cewa duk wanda baya siyasar gwamnati to cire hula ya fi wahala akan korar sa daga aiki, to su kori duk wanda suke son su kori su gani ai in su jahilai ne ba su san dokokin kasa ba, tsarin mulki bai hana duk wani mutun ba ya fadi ra'ayin sa ba. Kumu su jami'an tsaro da ka ce, a Najeriya ta yanzu zaman lafiyar su ne su bar jama'a su zabi wanda suke so ayi abin cikin adalci da kwanciyar hankali, babu jami'an tsaron da ke iya hana fitinar da za ta zo ida har aka samu wani abu akasin haka. Sannan babu hukumar zaben da ke iya hana jama'a su zabi wanda suke so, kuma idan har suka ce za su lalata abin da akayi to abinda zai biyu baya ba zai yi ma mutane kyau ba.

Friday, August 13, 2010

NAN KUMA MONDAY NE RIKE DA BIBLE ACIKIN MASALACI

GA SHI NAN A TATTARO MASA KAYAN SA DA KE CIKIN MASALACI ZUWA...

LABARIN MAYAUDARIN KIRISTA A KATSINA

Daga: Abdulkwanarya
A ranar Lahadi 8/8/2010 ne asirin wani mutum da ya musulunta a masallacin kungiyar Izala da aka fi sani da Kandahar Kofar Kaura Katsina tsawon shekara uku da ta gabata mai suna Monday wanda ya canja suna zuwa Ahmad ya tonu, bayan da ya safe shekaru ukun yana yaudarar masu kula da wannan masallaci ta hanyar karbar tallafi.
Yadda abin ya faru kuwa shine, wani dan acaba (kabu-kabu) ne ya dauko Monday daga wata Coci ya kawo shi wannan masallaci.Bayan ya ajiye shi ne, sai ya ga wannan mutum ya shige cikin masallaci, abinda ya cikashi da mamakin da ya kasa daurewa har sai da ya tambaya kodai akwai hanyar bi-ka-wuce ta wannan masallaci. an ba hi amsa da cewa babu wata hanya, masallaci ne kawai.sannan ya tabbatar masu da cewa ya fa dauko wani mutum daga Coci ya kawo shi nan kuma lallai yana nan cikin masallacin.Sai aka shiga da wannan dan acaba , ya kuma nuna Monday cikin masallacin gaban kayansa da dama anan cikin suke kuma nan yake kwana. A nan take aka caje shi ,sai aka sami wani Littafin da aka rubuta "Littafi mai Tsarki" akansa.
Yayin da aka tambayi Monday akan lamarin ya tabbatar da cewa, haka aka yi bai kuna musanta faruwar hakan ba sai dai ya ce, bai dade da komawa zuwa Cocin ba. An kuma tambaye shi mi yasa da ya koma Kiristansa bai bar masallacin ba? Sai ya yi shiru babu amsar da ta fito daga bakinsa.
Bayan musuluntar Monday, "har makaranta aka sama masa a Kaduna , amma ya ki ya halarta"inji Ustazu Sani Musa, a lokacin da yake kara bayani akan lamarin.
An yi kokarin mika Monday ga hukumar tsaron farin kaya,amma suka ce a bayar da shi ga hukumar 'yansanda, za su karbi batun daga bisani.
Wani da wannan Dandali na katsinawahausawa ya nemi jin ta bakinsa akan wannan lamari, ya bayyana abin da cewa akwai sakaci da bangaren yan gunkiyar da har suka kyale wannan mutum tsawon wannan lokaci ba tare da bin diddikin wadanda yake mu'amala da su ba" mi ya hana su binciki shi kowanene, danginsa da makamantan su don su san dawa suke mu'amala"a tabakain wannan malami.
Shin Monday dan leken asiri ne na kungiyar kiristocin Nijeriya (CAN) ko kuwa dan leken asirin wasu kungiyoyin ne na daban? Kuma hukumomin tsaron za su iya yi wani abu akan lamarin ? Tambayoyin da har zuwa aiko da wannan labari ba a sami amsoshinsu ba.