Wani Yaro dan shekaru ashirin da biayr mai suna Muntari Ibrahim da ke zaune a unguwar tashar gagare cikin garin katsina ya rataye kansa inda nan take ya mutu.
A wata wasika day a bari kuwa jami’in yada labarai na rundunar ‘Yan Sanda a jihar katsina ya nunawa manema labarai, Marigayi Muntari y ace ya dau wannan matakin ne domin yagaji da halin da yake ciki.
Marigayi Muntari ya kuma roki gafarr Iyayensa, ya kuma fada cewa akwai wani dinkinsa wajen wani taila idan an amsu to a baiwa mahaifinsa.
Mahaifin nasa Ibrahim ya fadawa wakilinmu cewa wani Yaro ne dai ya leka dakin kofar gida a inda ya ga Muntari a rataye nan take ya sanar da mahaifinsa shi kuma ya fadawa ‘Yan Sanda.
Alhaji Ibrahim wanda yake malamin makarantar All one y ace marigayi masanin Qur’ani ne kuma Yaro ne natsustse.
Ya ce marigayi ya dauki tsawon shekaru biyar bashi gida, inda bai dade da dawowa ba.
A cewar uban Yaro ya dawo gida cikin koshin lafiya, inda babu wata alama ta motsuwa a jikin sa, ko alamun yana shaye-shaye ko wani abu na damunsa.
Safiyar da zai rataye kansa said a ya zo dakin ya gaida ni, inji uban Yaron.
Jami’an ‘Yan Sanda ne suka cire igiyar day a rataye kansa sannan suka kai gawar Asibiti a inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.s