Monday, July 12, 2010

HABA! AL-AMIN CIROMA

Daga Mohammed Zaharadeen, katsina
Batu akan badakalar ‘yan fim da Malam Rabo abu ne da babu ranar da za’a daina tattaunawa akan shi, musamman a kafafen watsa labarai, kuma tarihi ba zai taba mantawa da shi ba.
Haka kuma akwai masu goyon bayan ‘yan fim akan sana’ar su amma basu tare da su akan sauran ma’amullolinsu na yau da kullin, sannan akwai wadanda su a wajansu ‘yan fim akan kowane irin mataki ba masu laifi bane, kuma ba za su taba yin laifi ba. wasu kuma na ganin akwai inda yakamata a gyara. Haka abin yake idan aka juya akan Malam Rabo wasu na ganin da gangan ne gwamnatin jihar Kano ta kawo shi domin ya takurawa ‘yan fim da harkar baki daya. Idan kuma ka dubi wani bangaren za’a ga wasu suna goyon bayan irin matakin da hukumar tace finafinai ta jihar kano ta dauka akan ‘yan fim cewa daidai ne idan da abinda yafi haka a kara.
Wannan tasa babu wata rana da zata wuce ba’ace wani abu ba akan wannan batu ba, haka kuma abu ne da ba zai taba gushewa ba a zukatan mutane musamman wadanda suke sane da irin wainar da ake toyawa tsakanin ‘yan fim Malam Rabo.
Idan har ba nayi kuskure ba, akan wannan batu ne Malan Aminu Ciroma yake son mutane da kansu su gane inda matsala take tsakanin Malam Rabo da ‘yan Fim daga nan sai a san wace hanya za’abi domin warwareta, ina ganin haka Ciroma ke son fayyacewa masu karatu irin mu.
Akan rigimar ‘yan Fim da Malam Rabo, ni a wurina duk abinda za’ace akan Malam Rabo wallahi bai da me ni ba domin nasan Rabo ba kanwar lasa bane. Haka kuma duk abinda za’ace akan ‘yan fim bai da me niba saboda suma nasan ba kanwar lasa bane.
Amma abinda nake son yin magana akai shi ne gaskiyar magana tun lokacin da na karanta rubutun Ciroma na farko mai take “Rabo da ‘yan fim a mahangar Ilimi” wallahi naji wani shakku akan wannan rubutu domin gudun kadda ciroma yayi aikin da ba na shiba ya yanke hukunci, ma’ana kadda ya kwafsa, dalilin na jin wannan tsoro shi ne ciroma ba dan Jarida bane amma ma’aikacine a kamfanin buga jarida a fanbaran na’ura mai kwakwalwa (computer operator) duk da cewar yan cikin wannan masa’anta hakan ba zai hana shi amfani da basira, ilimi da kuma hikimar da Allah ya bashi wajan yin wannan nazira ba domin masalahar wannan masana’anta wadda hatta wadanda ba cikinta suke ba suna son ganin irin wannan badakala ta kawo karshe tsakanin ‘yan fim da Malam Rabo, amma matsalar itace da wahala ya iya kiyaye dokokin aikin jarida wajan rubuta irin wannan labarin wanda ina da tabbacin sai da yayi dogon bincike kafin ya zauna ya rubuta shi (writing the investigative report or write-up).
Duk da cewar bani da tabbas akan mutane biyun da suka yiwa ciroma wasu tambayoyi ko martani yana da nasaba da rashin tabbas din da suke da shi na ganin da wahala yayi abinda yakamata yayi, wanda hakan yasa suka kasa barinka har sai rubutub naka ya kare kafin nan sai su yi maka duk tambayar da zasu yi maka. Amma kuma idan da zaka bi ka’idar aikin jarida ni bani da matsala ko shakko akan cewa ba zakayi adalci ba, sai gashi wadannan mutane biyu sun yi maka ingiza mai kantu ruwa ka fadi matsayar akan harkar Fim da sunan bada amsa tun kafin rubutun naka ya kare, inda nan ne duk wani mai tambaya ko martani yake da damar yi maka kai kuma ka bashi amsa ba tare da kame-kame ba.
Maganar da kayi da sunan bada amsa ga tambayar zan kawo da kuma amsar da ka bada inda nan ne nake ganin ka kwafsa, “ shin su ‘yan fim ba su da laifi ne? Idan suna da shi, me yasa ba mu ji ka na yawan yi masu tambihi ba? Ko kuwa don ka na daga cikin masu shirya finafinan ne”? wannan itace daya daga cikin tambayoyin da aka yiwa ciroma. Shi kuma ga amsar da ya bada “game da me yasa bani farfagandar laifin ‘yan fim, sai in ce maka, wata kila yau ka fara karanta ni ko shafina a wannan jarida. Idan ba haka ba, to ya na da kyau, ka waiwaya baya, domin kuwa zan yi alfaharin cewa tun da na fara ta ba yin rubutu a fannin finafinan Hausa a wannan jaridar, ban taba nunuwa a fili cewa wai ‘yan fim ba su da laifi ba. Idan mai karatu na biye da wannan shafin, nake jin, babu wata jarida da ta bada labarin badakalar da Maryam Hiyana ta yi, kamar Leadership Hausa”. Wannan kusan ince shi ne jigon amsar da ya bada, amma daga karshe ne dadin labari ya kwashe shi yake cewa “Acikin ‘yan fim, wallahi, zan iya dafa Alqur’ani cewa mafi yawansu, ba su san abinda ake kira Luwadi ko Madigo ba, kuma ba sa shaye-shaye, sannan uwa uba, ba sa yin Zina”. Ciroma wannan furuci da kayi a wurina ka rusa duk abinda kake kokarin fitowa da shi a fili domin jama’a su gane tsakanin Malam Rabo da ‘yan Fim a ina matsalar take?
Al-amin kayi hakuri, zan yi maka wata matshiya da wasu abubuwa da suka faru a farfajiyar shirin fim wanda yana da wahala kace baka son sun faru ba, koda baka son duka ba nasan kasan wasu, wanda hakan ya su daga cikin ‘yan fim suka aikata yasa ake kallon su da kuma danganta su da shaye-shaye, Madigo, Luwadi da kuma Zina, wanda kai kayi ikirarin cewa zaka iya dafa Alqur’ani mafi yawan ‘yan fim ba su ma san abinda ake nufi da kalmomin da na ambata ba gami da su, wannan a fili yake ka nuna kai dai indai akan ‘yan fim ne, sai dai akashe tsohowa kan daddawarta.
Abubuwa guda goma da zan kawo a wannan rubutu nawa zasu yi maka manuniya akan ‘yan fim da zaka dafa Alqur’ani akan su, daga nan sai masu karatu su yanke hukunci akan lamari. Kayi hakuri Ciroma cewa mafi yawan su, ni dauka kashi 70% cikin dari, basu san abinda ake nufi da wadannan miyagun halaye ba, ban san inda kake wadannan abubuwan suka faru ba har baka sani ba kuma ba’a baka labari ba, ko wannan ya nuna cewa kai ba dan jarida bane, marubuci ne kawai? Matashiya akanka kafin in fara bayanin sauran, ina iya tuna lokacin da Mujallar fim ta buga hotonka kana ba wata yar fim abinci a lokashin wanda hakan yayi matukar taba mutuncinka, sannan da yawan mutanan da suka san akidarka duk da cewa ...kai akidar ma kwamashiyal ka keyi, in baka sani ba, to ka sani, suna cin mutuncin masu iri akidarka da bada misalin wannan hoton naka da aka buga, da fatan ka tuna da wannan.
1 Abu na farko shi ne, zan fara da misalin abinda ya faru a garin da nake wanda duk wanda yake harkar fim a katsina yasan wannan maganar. Akwai lokaci da marigayi Ahmed S. Nuhu suka zo shotin katsina wata yarinya daga cikin yan fim din tayi satar hanya taje ta kwana dakin wani saurayi, washegari da ta dawo ya kamata ya zane ba wanda ya bashi hakuri sai wanda bai san abinda ya faru ba, ba yan fim din katsina kadai ke wajan ba har da na Kano wanda nasan in daya daga cikinsu ya karanta wannan labari zai tuno da lokacin, haka itama yarinya duk da cewar yanzu ta girma a harkar da anyi maganar zata tuna. Tambaya anan me ake nufi da kwana dakin wanin saurayi da wannan yar fim tayi a katsina?
2 Abu na biyu shi ne wanda duk duniya ta san shi, shugabanninyan fim na Kano sukayi taro sukace sun tsaida mafi yawancin ‘yan fim sakamakon laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa, laifuffukan sun hada da shaye-shaye, Madigo, Luwadi da kuma Zina. Haka kuma babu wani dan fim daga cikin wadanda aka tsaida da yace an bata masa suna ko anci mutuncinsa saboda haka yana neman hakkinsa a kotu. Tambaya anan ciroma yana nufin bai taba jin wannan labarin ba, duk da cewa jaridar da yake aikin tana daya daga cikin kafafen watsa labarai da ake dogaru da su?
3 Na uku shi ne, a Kano abin ya faru, marubuci Bala Makosa ya taba wani rubutu inda ya bayyana yadda ‘yan siyasa Malaman buge ke basu fatawar cewar idan har suna son biyan bukatar su to lallai sai sunyi Zina da fittaciyar ‘yan fim kafin bukata ta biya, Makosa ya bada hujja ne da cewar yan fim da abin ya faru da su ne suka bayana masa hakan. Tambaya anan ciroma bai taba jin wannan labarin ba? Inda yana da tababa ya tambayi Bala Makosa zai ji karin bayani.
4 Na hudu kuma, na taba kai ziyara ofishin wani mawalafin Mujalla a kaduna, muna cikin hira sai muka tabo maganr ‘yan fim, shi ne yake cewa, “ ni nasha fada cewa ‘yan fim ba za su iya kare kansu a waje na ba, bare a je wajan Allah sakamakon abubuwan da suke aikata” mai wannan maganar yasan harkar fim ciki da wajanta a duk fadin arewacin kasar nan. Daga nan yace “ka ga nan inda kake zaune”. Nace eh! To anan wata ‘yar fim ta zauna nake tambayarta ya sunan macen da bata kwana gidan iyayenta? Sai ta amsa da “mai dabi’ar karuwa” sai yace mata da yawan mata ‘yan fim haka suke, ya kara da cewa kuma bata yi gardama, sannan fitacciyar Jaruma ce ko wancen lokacin, kuma nasan da taga wannan rubutun zata iya tunawa. Anan me Ciroma zai ce akan wannan ‘yar tattaunawa?
5 Haka kuma akwai wata ‘yar wasa da take Kano da zama ana yi mata lakabi da ... ‘yar Madigo, kuma tana amsawa babu wanda ya taba cewa me yasa take amsawa, sunan ‘yar wasan ya fara kalma “Z” sannan ina da tabbacin cewa Ciroma yasan wannan yarinyar idan ma har bai santa ba, to ita ta sanshi kuma har yanzu tana cikin wannan masana’anta ana damawa da ita. Ina mai ba Ciroma tabbacin cewa idan yanzu ya hadu da wannan ‘yar wasa da ya kirata da wannan sunan zata amsa kamar yadda inda nace Al-amin Ciroma zai yi wuf ya amsa da cewa na’am.
6 Baya ga wannan a garin kaduna, acikin wata mujallar da ke bada labarin ‘yan fim suna Gidauniya Alhaji Yakubu Lere ya taba bada labarin cewa wata ‘yar wasa mai Suna Ismuha ta haukache sakamakon shan miyagun kwayoyin da take ba dare ba rana. Kuma wannan labarin babu wanda bai san shiba. Zanyi mamakin cewa Ciroma bai san da wannan labarin ba, alhali yana cikin garin kaduna.
7 Abu na bakwai shi ne, wata ‘yar wasan da yanzu idan aka lisafa jerin masu tashe to dole ta zama ta biyu ko ta uku, abu ya faru dasu ita da babbar aminiyarta a garin katsina, amma labarin ya cika garin Kano kamar can ne abin ya faru. Yadda abin ya faru duk shekara ‘yan fim sukan zo Gala katsina wannan ya basu damar ko ba gala ba sai su niki gari zuwa katsina domin shakatawa, suma wadannan aminnai guda biyu haka ta faru da su, a wani hotal da ake Kira Zanburush hotel da ke katsina, inda wasu daga cikin abokan sana’ar su suka kai masa ziyarar bazata suna bude dakin sai kawai aka gansu, daya saman daya kwanciyar mace da namiji, haka kuma kwanan nan mujallar fim ta kara bada labarin daya daga jarimar da abin ya faru da ita cewa ana zarginta da tara mata gidanta, amma sai ta bada wani dalili na zaman su gidan nata. Abinda ya faru a katsina yasa kungiyar masu shirya finafinai ta Moppan reshen jihar katsina ta raba wata takardar cewa ba yarda a kara ba wani dan fim koma daga ina yake masauki ba, har sai ta amince a kowane hotel da ke cikin garin katsina haka kuma masu hotal suka amince da wannan doka ta Moppan. Zan so Ciroma ya kara fadada yadda yake samun labarai gami da ‘yan fim daga ko’ina cikin fadin arewa domin kadda ya rika fakewa a garin kaduna da Abuja ya rubuta san ransa.
8 Na takwas shi ne , da wani babban yaron Maryam Hiyana ya fada cewa don me yasa aka dora karan tsana akan Maryam ita kadai, abinda tayi babu wata ‘yar fim da batayi hakan ba, ko don su ba’a dauka ba a waya ana turawa mutane? Kuma shi wanda yayi wannan maganar babu abinda za’a boye masa a wannan harkar domin da shi ake yinta tuntuni. Kuma ina da tabbabcin Ciroma yasan wannan yaron na Hiyana in kuma bai Sani ba ya tambayi masu aiko masa da labarai daga garin Kano domin cikeken bayani akan wannan furuci na shi.
9 Abu na tara wanda shi ne na kusa da na karshe cikin abubuwa goma da nace zan lissafa, kwanan nan ne mujallar fim ta buga wani labari wanda ina da yakinin Ciroma ya karanta in ma bai karanta ba wani ya bashi labarin, hukumar hada fatauci da shan miyagun kwayoyi ta kai wata ziyarar ba zata gidan ‘yar wasa Safiya Musa inda sukayi awan gaba da wasu daga cikin yaranta, wanda hakan ke nuna ko Safiya bata shaye-shaye tana daure wasu gindi suna yi.
10 Nagoma wanda shi ne duk lokacin da na tuna da shi sai naji cewa inda babu harkar fim da abinda ya samu wannan baiwar Allah da bai same ta ba. Wata ‘yar wasa da ake yiwa lakabi da “Beauty” wanda ina cewa kowa yasanta a harkar fim ta shaida mani cewa, babbar nadamarta a wannan harka shi ne tayi ciki kuma ta zubar da shi wannan al’amari yana matukar tada mata hankali a rayuwarta ta duniya kuma gashi bata san yadda zata yi ba tunda ta kashe rai. Wadannan abubuwan ba suke nan ba a’a na dai takaita su ne zuwa goma domin Ciroma ya kara samun haske akan tambayar da zan yi masa daga karshe akan furucin da yayi da dafa Alqur’ani akan ‘yan fim.
Ciroma wadannan abubuwan da na lissafa na daga abubuwan da mafi yawan jama’a suke dogaru da su wajan danganta ‘yan fim da wadancan miyagun halaye wanda kai kace kashi 70% ba su ma san abinda ake kira da wannan sunaye ba. Gaskiyar magana naga kuskuranka akan wannan furuci da kayi, domin ni a zatona ko Dictionary aka baka, ba zaka taba yarda ka dafa ka yi shaidar mutanan da ba kowane lokaci kake tare da su ba, amma ba zan yanke maka hukunci ba har sai ka amsa mani wadannan tambayoyi guda biyu.
1 Ciroma wane irin Alqur’ani ne zaka dafa akan cewar ‘yan fim kashi 70% basu ma san abinda ake zargin su da aikatawa ba? Duk da kace dafawa zakayi ba rantsewaba, ina ganin kamar baka san banbancin rantsuwa dafa Alqur’ani ba, shi Alqur’ani kana iya rantsewa da shi ko da baka taba shi ba ma damar kayi imani da shi ba sai ka dafa ba.
2 wadanne ‘yan fim ne zakayi rantsuwa akansu na Kano, Kaduna, Katsina koko ‘yan fim din Hausa baki daya?
Idan har kabani amsa akan wadannan tambayoyi to kana da uziri a wajena kuma zan goyi bayanka ka dafa Alqur’ani, shin dafawa ko rantsuwa? Daga karshe kuma in ka kammala da wannan rubutun naka mai taken “Rabo da ‘yan fim a mahangar Ilimi” abu na gaba da zakayi rubutu akan shi shine me yasa mutane suke yiwa ‘yan fim kudin goro? A maimakon idan mutun daya yayi laifi to abin ya tsaya kansa shi kadai maimakon ya shafawa sauran.
Daga Mohammed Zaharadeen, katsina
08062212010/07027129735
katsinawahausawa@yahoo.com
www.katsinawahausawa.blogspot.com

No comments:

Post a Comment