Thursday, August 19, 2010

HIRAR MASARI AKAN KOMARWARSA CPC A KATSINA

KH: A da kana jam'iyyar PDP wanda kuma kana da matukar tasiri, sai gashi lokaci guda ka kuma CPC babu shakka ba za ka rasa dalili ba?
MASARI: To da farko dai kamar yadda jam'iyar PDP ta gudanar da zaben ta a 2006 ta kuma fitar da 'yan takarar ta duk kasar Najeriya, yadda kuma sauran jam'iyyu suka bi sawun yadda jam'iyyar PDP ta yi na kama karya. Bayan mun sauka muka ce to ya kamata mu bullo da wata hanya wadda za ta gyara tsarin mulki da zai fidda zababu bi sa ka'ida, har ma akwai wata kungiya da muka kafa G20. To mun yi kokari a wannan lokacin manyan ta matsa har aka zo aka yi convension har aka gyara wasu al'amurra na tsarin mulki wanda za su fitar da ciyaman na kwamitin amintattu.
To amma wadanda suka amshi mulki sai suka fi da lalacewa, a hankali- ahankali tun wurin zaben muka ga abinda ba su mukayi tsammani ba, bayan an aje akwatina sai daga baya aka ce wai anyi yarjejeniya duk sun ci ni kuma na san zaben shugaban kasa kan shi ko mutun daya ne ya fito sai an je fasa kuri'a idan ku ce ba su san shi to dole a canza dan takara amma wannan karan a jam'iyyar PDP mai mako ta bada mafita sai ya kasance ita ce ma matsalar, sai ka ga gwamnoni sun dauke aikin jam'iayya, idan gwamnoni suka fito suka ce zasu yi kaza sanna sai shugabanin jam'iyyar PDP su ce to, sai ya kasance wutsiya ita ke kada kare ba kare ne ke kada wutsaya ba.
KH: Yanzu idan na fahimce ka, dalilin da yasa kuka bar wannan jam'iyyar kamar kuna babu adalci acikinta ne yasa kuka barta?
MASARI:Absolute. Duk hanyoyin da muka bi wanda zai kawo tsarin da zai yi adalci acikin maganar na karshen nan shi ne wanda muka kawo sauran gwamnoni da yaran su da ke c ikin jam'iyyra suka watsar, kuma ya kasance nine gaba-gaba wajen wannan gyara, gyara bai yi nasara ba, shi ya sa nayi abin da ya dace dole idan da zan bar PDP ne saboda abinda aka yi min da na bari tun shekara hudu da suka wuce, amma ban bari ba.
KH: Amma me yasa ka zabi komawa jam'iyyar CPC duk da cewar akwai wasu jam'iyyun da dama?
MASARI: Ita jam'iyyar CPC wadanda suka kafa ta, irin matsalolin da muka fuskanta a jam'iyyar PDP suma irinta suka fuskanta a jam'iyyar su suka bar ta suka kafa CPC mai akida, wanda kuma mu akidar muke son a bi, saboda haka idan ace ga ka'idar jam'iyya na bi, aka zo akayi jarabawa a matsayin 'yan takara ni da kai, ta nuna jama'a sun fin sonka shi kenan sai in mara maka baya, ai daman ga ka'idar, amma da rana kiri-kira aka baka kuma daga baya ace in zo in bika ai abin ya zama bauta kuma ni na gaji da ita.
KH: Amma gashi ita wannan jam'iya sabuwar jam'iyyar ce, ka na ganin alamun zata yi tasiri a siyasar Najeriya?
MASARI: Ba yawan jama'a sune kasuwa ba? Kai ka ga taron da akayi anan, ka ga motoci da mutanan da suka zo tunda daga sabuwa har Mai'adua, ka gani ko? Indai ba PDP za ta yi kwace ba, kuma a wannan karon ka ji abin da mutane suka ce sai dai akwata bisa ran su.
KH: Misali yanzu kana da wani ra'ayi na tsayawa takara, ko ba ka kai ga yanke shawara ba?
MASARI: Gaskiya yanzu ban yanke wata shawarar tsayawa takara ba.

No comments:

Post a Comment