Thursday, August 19, 2010

TATTAUNAWAR MU DA DAKTA MUSTAPHA INUWA, TSOHON SAKATAREN GWMANTIN JIHAR KATSINA AKAN KOMAWARSA CPC

Tambaya: Dakta Mustapha da farko za mu so muji dalilin ficewarka daga jam'iyyar PDP?
DAKTA: To, dalilin dai kamar yadda muka sha fada wurare daban-daban shi ne rashin adalci da gwamnan jihar katsina Ibrahim Shehu Shema da makarabansa suke yi, a yadda suke tafiyar da harkokin jam'iyya da ita kanta gwmanatin jihar katsina.
Jam'iyya dai ya kamata ace ta kowa-da-kowa ce shi yasa ake ce mata PDP power, amma sai muka ga an maida Shema political Party saboda an zo an zauna duk wani wanda yana da hannu wajen haihuwar jam'iyyar da kuma raya ta ta hanyoyi da dama daga 1998 zuwa yau amma Shema ya zo ya nuna baya bukatar shi ya jawo wasu mutane ya ce sune za su? tafiyar da harkokin siyasa. Ya zo ya rushe kwamitin zartarwa na jam'iyya tun daga matakin gunduma har zuwa jaha, ya na da wadanda ya ga dama acikin ofis din shi, to wanna yasa muka nuna ba mu yarda ba, ba taimako bane ga jam'iyya, a rushe ayi kamar yadda doka ta tsara, sannan muka bi duk matakin da ya kamata mu bi anan jiha muka kai koke tarayya, daga karshe ta tabbata ba, sai muka fahimce Shema nema yake ya kashe jam'iyyar PDP mu kuma ba za mu so a kashe ta ba muna ciki.
Dalili na biyu shi ne ita dai jam'iyya amfanin ta idan an kafa gwamnati to ta taimaka ma jama'a, musamman alkawarin da aka dauka lokacin zabe, da dama Shema muka zagaya muka roki jama'a domin a zabe shi za a yi masu ayyuka na alheri, wadanda suka shafi kowane bangare, sai mu ka ga shi Shema ba wannan ya da me shi ba sai manyan ayyuka musamman hanyoyi har da inda ba a bukatar hanya.
An bar mutane babu ruwan sha, babu magani, makarntu daliban sun koma almajirai, an ki daukar malamai, musamman na karkara an sa kananan hukumomi sun gina an ki daukar ma'aikata, sai mu ka ga babu dalilin da sai sa mu ba wannan gwamnati goyan baya, to sai muka bai kamata ba mu cigaba da zama cikin wannan jam'iyya saboda babu wani aiki da a ka yi wa jama'a ba re aba da misali da shi har a sake zabar ita wannan jam'iyya, to wannan da ma wasu dalilai da dama ya sa muka fita daga PDP.
TAMBAYA: Ba ka gani irin manyan ayyukan da ya yi kamar yadda kace; kamar hanyoyi da gidaje da ya yi wanda har ana ta bashi kyaututika, ba ka ganin wannan nasara ce wanda kuna iya duba al'amarin?
DAKTA: Su wa? Wadanda suka san matsalolin mutanan katsina koko? Wadanda suke bada irin wadannan kyaututikan idan ka bincika ba wanda ya taba zuwa katsina, wadannan kyaututinkan biya ake ana bada so da daman su, kuma kyautar da ya amsa ta farko ba ta aikin sa ba ce, akin da mukayi ne na farko domin an bata ta ne 2006 ba ta shi ba ce ya karba amma daga lokacin zuwa yanzu wace kyauta ya karba? Amma a zahiri mutanan da ke katsina su suka son halin da ake ciki, yanzu idan ka je asibiti ba magani lokacin gwamnatin da ta shude ana sayen magani na Naira miliyan dari hudu, amma yanzu na miliyan arba'in ake saye, gashi ba ruwan sha ba a dauke ma'aikata aiki ba.
Ga shi kananan hukumomi ba sa iya komin sai abinda gwamnatin jiha ta ce masu, komi Ciyaman zai yi sai ya neman izini a jiha kuma daga can za a bashi dan kwangilar da zai yi aikin, amma maida kusan mutun biyu sune ke yin kwangilar ayyukan kananan hukumomin jihar katsina, magana ce ta gaskiya sai dai mutane ba su son a fadi domin tsoro ko wani dalili, ko su Ciyamomin tsakani da Allah ba su jin dadin wannan gwamnati suke ji ba, an maida kamar almajirai saboda babu wani aiki da suke, kuma za ka ga kananan hukumomi suna samun kudin da basu kasawa miliyan ashirin ba bayan sun biya albashi amma me ake da su? Dan abin da za a ba su daman da ta so kishirwar sun wawure. Maganar ace ana bashi award a je 'yan Abuja su zabe shi, idan kuma maganar zabe ne kai ka sani mutane sun gaji da gwamnatin shehu ba za su sake zaban ta ba.
TAMBAYA: To, mutane da yawa suna ganin shigowar ku CPC ya yi za kuyi ku amshi wannan gwamnati?
DAKTA: To, ba jama'a ke zabe ba? Insha'Allahu jama'a za su zabe gwamnatin CPC kuma ba wai jihar katsina kadan ba, daman su ke zabe.
TAMBAYA:Kana ganin yanayin zaben zai canza ganin yadda ake zabe a baya?
DAKTA: Karma ya canza, mutane su za su canza shi da kan su, ace wai anyi sabuwar doka duk wannan ba shi bane, in jama'a na son su ci zabe za su ci, ai anyi anan jihar ba wainsaia anje nisa ba, anan katsina 2003 anyin zabe mun fadi, Sanatoci biyu muka rasa cikin uku, 'yan majalisa takwas muka rasa cikin sha biyar, inda zaben farko aka fara anan jihar na gwamna Umaru da baiyi second term ba, kuma wahalar da mutane suke cikin yanzu ita ta sa suka ce ko za su mutu sai dai mutun amma sai sun tsare mutuncin su a wannan karon daga wannan wulakantatar gwamnati.
TAMBAYA: A karshe wane kira za ka yi ga masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro da kuma ita kanta hukumar zabe ta kasa domin tabbatar da anyi zabe cikin adalci da lumana?
DAKTA: Ni kira zanyi ga dukkan jama'a, musamman sakunan mu da suka zu bar ma kansu da mutunci, suna abinda yake mutane fa ba su jin dadin sa, ya kamata su tsare mutuncin su, su tsare girman su, su dauke kowa na su ne, duk wanda Allah yasa aka zaba to na su ne, amma ace sakuna suna bada umarni kiri-kiri suna ga ya ma jama'a ga gwamnatin da suke so, to wannan kuskure ne.
sannan akwai jami'an hukumar kananan hukumomi suna za ga yawa suna gaya wa mutane cewa duk wanda baya siyasar gwamnati to cire hula ya fi wahala akan korar sa daga aiki, to su kori duk wanda suke son su kori su gani ai in su jahilai ne ba su san dokokin kasa ba, tsarin mulki bai hana duk wani mutun ba ya fadi ra'ayin sa ba. Kumu su jami'an tsaro da ka ce, a Najeriya ta yanzu zaman lafiyar su ne su bar jama'a su zabi wanda suke so ayi abin cikin adalci da kwanciyar hankali, babu jami'an tsaron da ke iya hana fitinar da za ta zo ida har aka samu wani abu akasin haka. Sannan babu hukumar zaben da ke iya hana jama'a su zabi wanda suke so, kuma idan har suka ce za su lalata abin da akayi to abinda zai biyu baya ba zai yi ma mutane kyau ba.

1 comment:

  1. ¬ hal yg tidak pernah terbayangkan kini menjadi kenyataan,dengan keluarga saya untuk AKY SANTORO kami ucapkan banyak terimah kasih karna berkat BANTUAN AKY SANTORO ALHAMDULILLAH keluarga kami bisa lepas dari segala HUTANG HUTANG. karna nomor togel yang di berikan KY SANTORO YAITU-4D. nya BENAR BENAR TERBUKTI TEMBUS 100% DAN SAYA MEMENANGKAN.125 juta.ALLHAMDULILLAH saya bisa menutupi semua tuhang hutang saya.dan MOTOR saya yg dulunya aku gadaikan,kini sudah di tebus kembali.dan kami juga sudah membuka usaha kecil kecilan,kami tidak menduga KY SANTORO TELAH MERUBAH NASIB KAMI DALAM SEKEJAP.dan hanya AKY SANTORO Lah DUKUN TOGEL YANG PALING BERSEJARAH DI KELUARGA KAMI.ini adalah benar benar kisah nyata dari saya.dan saya tidak malu menceritakannya.semua tentang kesusahan yg perna saya jalani.karna di situlah saya mulai berfikir bahwa mungkin masih banyak saudara kami yg membutuhkan bantuan seperti saya.yang ingin seperti saya silahkan hub AKY SANTORO DI NOMOR(_0823_1294_9955_).DI JAMIN 100% TEMBUS.JIKA ANDA PENUH KEPERCAYAAN DAN KEYAKINAN SILAHKAN ANDA BUKTIKAN SENDIRI.DAN SAYA SANGAT YAKIN BAHWA ANGKA GHOIB YANG DI BERIKAN KY SANTORO DAPAT MERUBAH NASIB ANDA SEPERTI SAYA.SEBELUMNYA SAYA MOHON MAAF KALAU ADA PERKATAAN SAYA YANG KURANG SOPAN.TOLONG DI MAAF KAN.TERIMAH KASIH.THANK'Z ROOMX ZHOBATH.!!!

    ReplyDelete