Thursday, August 19, 2010

MARTANIN DA ALH SABO MUSA YA MAYAR MA 'YAN CPC A KATSINA

wannan ita ce tattaunawar da wakilinmu da ke katsina ya yi da shugaban kungiyar tuntuba akan sake tsayawa takarar Gwamnan jihar katsina Barista Ibrahim Shehu Shema a katsina.
Alh. Sabo Musa yana daga cikin manyan 'yan siyasar jihar katsina yanzu,ya fadi dalilin kafa wannan kungiya ta so mai suna Shema partinership, sannan ya maida martanin akan zargin da jam'iyyar CPC ke yiwa Sarakunan katsina da jam'iyyar ta CPC ta ce sun atsoma baki cikin al'ammuran siyasar katsina, dama wasu bayanan ga yadda hirar take:
KH:Sabo musa kayi man bayani dalilin kafa wannan kungiya ta ku da kake yi wa jagoranci. Wanda kuma an kafa ta ne domin a ga gwamna Shema ya sake cin zabe a shekarar 2011?
SABO MUSA: gaskiya kamar yadda ka sani makasudin kafa wannan kungiya don mu sakawa shi gwamna, bisa ayyukan alherin da yake gabatrwa a jihar ta katsina. Ya kamat duk wani mai kiyasa a katsina, yasan irin abin da Shema ya yi wannan ne yasa muka hadu muka kafa wannan kungiya domin yin wani abu da zai nuna masa cewa mu mutanan katsina mun ji dadin abin da ya yi. Sannan mun lura gwamnati tana aiki amma mafi yawancin mutane ba son abin da ake ciki ba.
Dalili ba biyu shi ne akwai wasu 'yan mara sa kishi duk da cewa sun shiga gwamnati sun tara kudi, amma kuma ba su son irin abin da shi gwamna shema yake a karkashin gwamnantin shi saboda hassada, suna ganin su yakamata ace suke yi kuma ba su ke yi ba. Sai suka rika amfani da dukiyar suna haddasa fitinu. Wannan yasa duk lokaci da suka soke shi mu rama idan sukai masa sharri mu nunwa jama'a wannan abun ba haka yake ga yadda yake.
Abu na uka kuma shi ne, za mu son ya cigaba da zama gwamnan jihar katsina, idan aka samu can jin gwamnati mun shiga cikin wani irin hali, saboda irin abin da ya yi ba a taba samun gwamnan da ya iske aiki sai da ya ida sannan ya cigaba da na shi, ka ga hanyoyi da ya fara yin wadanda za su kewaye gari, ga kuma gidaje da ya gina idan har aka samun can jin gwamnati ana iya kashe irin wadannan manyan ayyuka. Bayan haka ga wasu ayyukan wadanda suna da matukar amfani ga jama'a, misali kamar Asibitin Turai yar'duwa da kuma Asibitin Kashi wanda masana suka ce duk Afrika babu irin ta, ga motocin tafi da gidanka wanda da amurika da finafinai kadai muke ganin su, hatta mutanan da ke cikin karkara suna afmana da wannan garabasa.
KH: To, amma sai gashi wasu 'yan siyasa suna ganin abun ba haka ne ba, ya yarda wasu 'yan siyasar da aka fara tafiya tare, wanda har wasu daga ciki suka fice daga PDP zuwa ta jam'iyya?
SABO MUSA: Wannan ba gaskiya ba ne, yau idan an kyautatama al'ummar jihar katsina ba a kyautatama wasu da ke tare da gwamnati ba anyi laifi? Saboda haka ita gwamnati ta al'ummar jihar katsina ce baki daya, tunda gwamnati ta al'ummar jiahar katsina ce idan aka kyautattawa wani ba a kyautattawa wani ba, ba a laifi ba. Wadanda suka bar jam'iyyar PDP suka kuma wata daman ba su yi ma jam'iyyar komi, duk wanda ke cikin PDP yake ya da manufar ta ba wata bukata tashi ta kashin kansa ba yana nan bai bar PDP ba.
KH: Gashi jam'iyyar CPC na zargin Sakunan katsina da tsuma baki cikin al'ammuran siyasa, musamman akwai wani sarki da ya nuna jam'iyyar da yake wane martani za ka maida akan wannan?
SABO MUSA: Ace Sarakunan mu suna jam'iyyu wannan cin mutunci masarautar mu ne da Sarakunan mu, wannan cin fuska ne ya kamata a daina. Sarakuna iyayen kasa ne, ra'ayi kuwa duk dan adam yana da na shi, yana son wane ya ci zabe, yana son wane saboda ayyukan alherin da yake ya zarce, saboda haka ra'ayi da ban siyasa da ban. Yau idan iyayen Sarakuna ba su ce Shema ya kyauta ba ai masu yi masa adalci ba, saboda ya kyauta din ya fito da mutuncin jihar katsina, ba a taba taimakon alhazai yadda ya kamata ba sai lokacin Shema, ba wata gwamnatin da ta taba gina masalatai da makarantu da kewaye makabarto ba kamar Shema, wannan aikin Sarakuna ne to sai gwamnati ta zo tana yin wannan don mi ba za su yabawa wannan gwamnati ba. Sannan ina kira ga kungiyar ma'aikata kadda su yarda ayi amfani da su, ko ace su nemi karin albashi, ko karin karamar hukuma ko neman jiha, sannan kadda a cuci ma'aikata amma kuma kadda su kuma su matsa su ce kan su suke so. Kamar ma'aikatan Asibiti da suka tafi yajin aikin ai ba su yi mutunci ba, ina kira a gare su da suji tsoron Allah shi aiki ba ana yin ba ne don albashi kawai, ana yin sa don taimako da samun lada. Saboda haka wancan kiraye-kiraye na CPC wannan abin je farwa ne, babu hujja babu ma'ana.
KH: To a karshe wane kira za kayi ga 'ya 'yam Jam'iyyar PDP su ga sun hada kawunan su domin gwagwarmaya mai zuwa a wannan zaben?
SABO MUSA: Mu 'yan jam'iyyar PDP kan mu hade yake, daman wadanda suke gefe suna ganin abin alheri ne garesu akafa wata gwamnati ai sun sa irin abin da suka aikata a kafa gwamnati su gani mana, yau mutanan nan duk abin da muke cikin gwamnatin nan da su muke ba su taba cewa PDP bata da gaskiya ba, sai yanzu ne za su zo su fadi yanzu ne PDP ba ta yi gaskiya? Bayan sun shiga gwamnati sun debi kudin jama'a to su maido ma gwamnati kudin ta mana, kuma ka tuba ba za kara yin abu be shi ne sharadin tuba, idan kuma kudi ne na wasu ka diba to ka maida masu kudin su sannan ka tuba. Saboda haka a karshe ina kira ga jama'ar jihar katsina gwamna shema ya yiwa mutane abin da ya da ce, mu fito mu saka mashi, duk farfaganda da wasu mutane keyi ku auna nagartar wadanda suka fito takara a wasu jam'iyyun ku gani mana, kuma sai ma ranar zabe za a kara ganin bambamcin shema da sauran.

No comments:

Post a Comment